Skip to content

Yadda ake miyar kuka yar Borno

miyar kuka yar borno
5
(2)

Ku koyi yadda ake miyar kuka ‘yar Borno ga dadi ga kuma kyau. Wannan miyar kuka ta musamman ce, ba irin miyar kuka ce da kuka sani ba.

Abubuwan hadawa

  1. Garin kuka
  2. Tafarnuwa
  3. Citta
  4. Nama gadon baya
  5. Tattasai da attarugu kadan
  6. Maggi
  7. Albasa

Yadda ake hadawa

  1. Ki yanka albasa ki dan soya sama sama ki sa nama a ciki da kayan kamshi da ruwa naman ya yi ta tafasa har ya dahu
  2. In ya dahu a tsame naman a daka a mai da shi cikin ruwan sa da ke kan wuta.
  3. Sai a yi jajjagen tarugu da tattasai da tafarnuwa da citta a zuba a ciki.
  4. A sa maggi a bari ya tafaso sai a kawo kuka a rika kadawa a hankali har ya yi kauri.

To sunan wannan miyar manta sunan ka. Mu dai ‘yan Borno da biski muke ci. Amma za a iya ci da kowani irin tuwo. Ni dai biski shi ne zabi Na. Sannan za a iya karanta: Lemon cucumber drink sauransu.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×