Skip to content

Yadda ake tuwon amala

Share |
Yadda ake tuwon amala
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ga yadda ake tuwon amala, mu koya ‘yanuwa. Sannin yadda za a dafa tuwon amala wani dama ce da ba za ki bari ya wuce ba. San an gwada…

Abubuwan hadawa

  1. Garin bawon doya kofi biyu
  2. Garin alabo( garin rogo) kofi 1
  3. Ruwa
  4. Tukunya
  5. Muciya

Yadda ake hadawa

  1. Ki tankade kofi daya na garin bawon doyan daban a wani kwano. Ki dauko garin alabonki kofi daya da garin bawon doyanki kofi daya sai ki hada su gu daya ki tankade a wani kwano daban.
  2. Ki daura tukunya akan wuta ki sa ruwa (daidai yanda tuwonki ba zai yi ruwa ruwa ba kuma bawai ya yi tauri ba) ki rufe tukunya nadan wani lokaci, sai ki dauko garin bawon doyan (wanda ki ka tankade kofi daya da farko) ki sa masa ruwa ki dama.
  3. Idan ruwan ya tafasa sai ki talga ki rufe nadan wani lokaci sai ki dauko garin alabon ki (wanda ki ka hadashi da garin bawon doyan) ki tuka ki rufe tukunyanki na dan wani lokaci kadan sai ki sauke ki sake tukawa ki kwashe a kula ko ki daure su a leda.

Ana ci da miyar egusimiyar ganye ko kuma da ko wacce irin miya ta yauki, kamar miyar kubewa da sauransu. A ci dadi lafiya

Karin bayani

Za ki iya tukashi ba tare da kinyi talge ba (yanda za ki yi shine ki hada duka garin bawon doyan ki da garin alabonki ki tankade su gu daya. Idan ruwan zafinki ya tafasa sai kina zubawa a hankali kina tukashi har sai ya hade jikansa ,sai ki rufe shi na dan wani lokacin ki sake tukawa ki kwashe a kula ko ki daure su a leda. Amma ki tabbatar bai yi gudaji ba.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×