Ku koyi yadda ake tsiren tukunya. Wannan tsiren tukunya yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Jan nama kilo
- Albasa 1
- Maggi 4
- Yajin barkono 1/2 cokali
- Kuli kuli (gari)
- Kayan kamshi
- Man gyada ludayin miya
- Koren tattasai 2
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki wanke namanki ki masa yanka mai fadi-fadi ki ajiye a gefe.
- Sai ki hada yajin da man gyada da garin kulikulinki ki sa maggi da kayan kamshi sai ki kwaba.
- Sai ki dinga shafawa a jikin naman gaba da baya.
- Idan kin gama sai ki kawo tukunya ko kasko (frying pan) mara kamu sai ki jera ki dora a wuta ki rufe ki barshi. Kar ki sa wutar tayi yawa.
- Sai ki ringa juyawa, idan yayi sai ki sauke ki yanka dai dai misali kisa sa pilet ki yanka albasa da koren tattasanki.