Skip to content

Yadda ake super soft cake

yadda ake super soft cake
0
(0)

Cake lovers ga wani cake nan na musamman da na zo muku da shi. Ba za ki gane ba uwargida amarya sai kin gwada wannan super soft cake din. Biyo ni ku ga yadda ake hada shi dalla dalla.

Abubuwan hadawa

  1. Sugar kofi 1
  2. Flour kofi 3
  3. Kwai 10
  4. Butter (sima’s) 1
  5. Baking powder 1/2 tspn
  6. Flavour

Yadda ake hadawa

  • Da farko za ki hada butter da sugar ki buga su sosai da muciya ko mixer.
  • Ki fasa kwai daya bayan daya kina sawa kina hadawa.
  • Idan kin ga sun hade sai ki sa flour da baking powder da flavour dinki.
  • A zuba a farantin gasa cake a yi pre heating na oven a gasa na tsawon mintina 45. 5.
  • Idan ya yi a cire a yanka, za ki iya topping da ko wane irin decoration ko ki zuba zuma ko chocolate.

To mai karatu wannan shi ne yadda ake hada wannan super soft cake. Sai mun hadu a girki na gaba,kafin nan za a iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake valentine cut-out cookies da nakamantansa.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×