Skip to content

Yadda ake spring rolls

Share |
yadda ake spring rolls
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku biyo ni mu koyi yadda ake spring rolls. Assalam alaikum barkanmu da war haka.

Abubuwan hadawa

Dough

  1. Filawa
  2. Gishiri
  3. Ruwa

Fillings

  1. Cabbage
  2. Tarugu
  3. Albasa
  4. Lawashi
  5. Seasoning na maggi

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki samu bowl ki zuba flour da dan gishiri sai ki kwaba shi da hannun ki kaman yadda ake hada fulawar meat pie za ki buga shi sosai har filawar ta hade jikinta.
  2. Sai ki yi rolling dinta da fadi kaman circle. Ki ajiye a gefe har ki yi ma sauran fulawar haka gaba daya.
  3. Ki shafa mai akan daya sai ki barbada fulawa akai sai ki sake dora wata kuma akai.
  4. Haka za ki yi har ki dora su baki daya sai ki sake saka rolling pin ki hade su.
  5. Ki dora wannan fulawar akan non stick pan na tsawon mintina biyu ki dan bata tsoro.
  6. Ki sauke ki cire su daya bayan daya a hankali ba tare da kin bari ya balle ba.
  7. Ki sa dakakken tarugu da dan green pepper kadan da sauran kayan hadin baki daya banda cabbage.
  8. Ki dan juya su sannan ki sa cabbage dinki ki rufe. Bayan minti daya ki sauke dan kar cabbage ya yi Ruwa.
  9. Ki dauko ko wane circle na dough daya ki saka fillings na ki ki sa paste ki rufe gefen.
  10. Sai ki soya spring rolls dinki, shikenan komai ya kammala.
    Wanna shine yadda ake spring rolls, mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake hada watermelon smoothie da yadda ake coconut cupcakes da sauransu duk anan Bakandamiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×