Skip to content

Yadda ake samosa da spring rolls

Share |
yadda ake samosa da spring rolls
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake samosa da spring rolls mai dadi ga kuma kyau. Wannan method na yin samosa da spring rolls din yana da saukin hadawa.

Abubuwan hadawa 

  1. Flour 500g
  2. Gishiri pinch
  3. Man gyada 1tablespoon
  4. Ruwa
  5. Carrots
  6. Nama
  7. Cabbage
  8. Green beans da peas
  9. Seasoning da kayan kanshi
  10. Rosemary, parsley, bay leaves, albasa, attaruhu (jajjage)
  11. Man gyada na suya

Yadda ake hadawa 

Shi samosa da spring rolls ana bin hanyar biyu ne wajen hadasu; Batter method da kuma Dough method

Anan zamuyi amfani da dough method ne.

  1. Zaki samu bowl dinki mai tsafta ki auna flour din a ciki kisa gishiri da man gyada cokali daya sai ki kawo ruwa kina zubawa sai kina kwabawa kar yayi tauri kuma kar yayi ruwa.
  2. Za ki kwaba shi har sai ya dena kama miki hannu sai ki rufe shi na sawon mintuna dough dinki ya huta.
  3. Dough dinki na hutawa sai ki samu Mai kar ya wuce cokali daya zuwa biyu ki sa a tukunya ki daura a wuta kikawo jajjagen citta da tafarnuwa idan ya soyu ki sa jajjagen. Ki sa ki kawo sinadarin dandano ki sa ki soya ya shi ki sa dan sa ruwa kadan ki kawo yankakken carrot, green beans kisa. Note: Za ki tafasa green beans, carrots da peas idan baka so su canja kala kidansa baking powder a tafashen.
  4. Sai ki kawo su carrot dinki ki zuba, ki sa su parsley da rosemary kadan kadan sai ki barshi ya har sai wannan dan ruwan da kika sa ya shanye. Sai ki sauke ki barshi yana hucewa.
  5. Sai ki dauki dough dinki ki sa mu rolling pin dinki da board mai tsafta sai ki gutsira su dai dai ki dan barbada gari flour sai ki murza shi yayi round ya yi flat wato fale fale.
  6. Ki samu frying fan nonstick ki sa a wuta ya yi zafi sai ki sa shi ya dan gasu ki juya bayan shima yadan yi sai ki cire.
  7. Amma idan kina so ki ragewa kanki aiki most especially idan mai yawa za ki yi bayan kin murza na farko sai ki shafa mai a kai sai ki barbada flour kadan ki sake murza wani ki daura akai. Ni ina hada guda biyar.
  8. Sai ki dauko rolling pin dinki ki murza su su zama guda daya. sai ki gasa ki cire shi sai ki zo ki kama bakin za ki ga yana rabuwa da juna ki cire shi daya bayan daya ki sake jera shi bayan kin gama, ki sa wuka ki yanka shi gida hudu tunda round ne ko wani daya shine zaki yi samosa pocket da shi.
  9. Sai ki dauko flour kidan hada ta da ruwa da ita zaki dinga manne aljuhun da shi kamar yanda ki ka sani shape din triangle ne da samosa idan kin manne da filling ki sai ki zuba fillings dinki ki nane bakin.
  10. Ki sa mai na suya a wuta ya yi zafi sai ki fara soyawa. 

Note:

Banbanci samosa da spring rolls sune kamar haka:

  1. Shi samosa filling nashi da nama, shi kuma spring rolls cabbage ne da carrot da jajjagen kayan miya soyaye.
  2. Yankan cabbage na spring rolls dogaye ake yi, shi kuma samosa dicing ake yi.

Shi ke nan, a ci dadi lafiya 

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading