A yau kuma zamu duba yadda ake hada samosa, a baya mun yi bayani akan hadi na watermelon milkshake, za ki iya dubawa kafin mu ci gaba.
Abubuwan hadawa
dough
- Filawa
- Gishiri
- Ruwa
fillings
- Nama
- Tarugu
- Albasa
- Lawashi
- Seasoning na maggi
Yadda ake hadawa
- Farko za ki samu bowl ki zuba filawa da dan gishiri sai ki kwaba shi da hannun ki kaman ydda ake hada fulawar meat pie za ki buga shi sosai har fulawar ta hade jikinta,
- Sai ki yi rolling dinta da fadi kaman circle. Ki ajiye gefe har ki yi ma sauran fulawar haka gaba daya.
- Ki shafa mai akan daya sai ki barbada fulawa akai sai ki sake dora wata kuma a kai. Haka za ki yi har ki dora su baki daya, anan sai ki sake saka rolling pin ki hade su.
- Ki dora wannan fulawar akan nonstick pan na tsawon mintina biyu don ki dan bata tsoro. Ki sauke ki yanka shi gida hudu.
- Don yin fillings, ki dafa nama sai ki daka shi ko ki yi amfani da mince meat, ki sa a pan ki sa dakakken tarugu, da sauran kayan hadin baki daya. Bayan yan mintina idan ya dai daita sai ki sauke.
- Ki dauko ko wane side na dough daya ki saka fillings naki ki sa paste ki rufe gefen (yadda za ki hada paste shine za ki hada flour da ruwa ne yayi kauri).
- Sai ki soya samosa dinki shikenan
Mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake watermelonsmoothie da yadda ake butter creamicing dasauransu.