Mu koyi yadda ake miyar taushe cikin sauki, abubuwan hadawa guda takwas, matakai guda goma sha biyu.
Abubuwan hadawa
- Dafaffen nama da soyayyen nama
 - Alayyaho da yakuwa (ki wanke da gishiri ki sa a colender ya tsane)
 - Markadadden gyada (irin na kunun gyada)
 - Albasa
 - Grated tarugu da albasa
 - Maggi da gishiri
 - Kayan yaji (spices)
 - Manja da man gyada
 
Yadda ake hadawa
- Ki sami wukanki ki yanka dafaffafen namanki kisa a gefe
 - Sai ki dauko gyada ki kisa mata ruwa ki dama ta, itama ki ajiye a gefe
 - Sannan kisa tukunyarki akan wuta kisa manja da man gyadarki
 - Sai ki dauko albasa kisa, amma ki soya shi sama-sama
 - Yanzu sai ki dauko namanki da kika yanka kisa aciki ki soya sama-sama
 - Sai ki dauko grated tarugunki kisa aciki sannan ki juya
 - Ki kawo Maggi da curry da kayan yaji (spices) ki sa
 - Bayan haka, sai ki kawo soyayyen namanki ki sa sai ki juya
 - Sai ki tsaida ruwa kadan ki rufe tukunyarki na dan wani har sai kin ji ya fara tafasa
 - Sannan sai ki dauko ganyen ki kisa aciki ki juya ki rufe shi na dan wani lokaci
 - Ki dauko gyadarki (wanda kika dama) kisa aciki, sannan ki juya miyarki ki sake rufewa ki barta na dan wani lokaci
 - Daga karshe, sai ki sauke miyan ki
 
Zaki iya ci da couscous (kamar yanda kika gani a hoto) ko kuma da tuwon shinkafa ko semo da makamantansu.

