Yau zamu koyi yadda ake hada sinasir ne. Mu gyara zama ga yadda ake yi.
Abubuwan hadawa
- Farar shinkafa
- Tuwo/dafaffiyar shinkafa
- Yeast
- Sugar
Yadda akehadawa
- Za ki gyara ki jika shinkafa kamar na awa daya haka nan for.
- Sai ki kawo tuwon ko shinkafa daffafiya ki zuba ciki, ki sa yeast ki nika (amfi son nikan gida).
- Sai ki kara yeast rabin cokali. Kar ya yi ruwa kar kuma ya yi kauri sosai. Ki rufe ki ajiye wuri mai dumi.
- Bayan mintuna talatin (30 minutes) zai tashi ya dawo kamar kumfa, sai ki dora nonstick frying pan a wuta ki shafa mai ki rinka zuba kullun ki na rufewa. Da ya dahu za ki ga ya yi holes, haka za ki yi har ki gama.