Miyar kubewa danya miya ce da ta shahara ….. Miyar kubewa danya wata nau’in miya ce ta gargagjiya a kasar Huasa wadda ake yin ta da danyan kubewa maimakon busasshe. Ana amfani ne da ita kubawa danya bayan an wanke shi kuma an yanka shi kanana ko har ma daka shi a turmi da kanwa ko a markada a inji, wanda hakan ke sa miyar tayi yauki sosai.
Ana dafa miyar kubewa danya da kayan hadi irin su nama, ki (danye ko busasshe), albasa, tarugu, da manja(idan ba da miyar romo za’a ci sa ba). Haka kuma ana iya kara daddawa ko ogiri domin kara dandano.
A al’adar Hausawa, ana yawan cin miyar kubewa danya ne tare da tuwo kamar su tuwon masara, tuwon semombita, tuwon dawa, tuwon shinkafa harda ma sakwara. Miyar na da matukar amfani ga lafiya saboda sinadarai da ke cikin ita danyar kubewar. Akwai sinadarai irin su fiber wanda take taimakawa wajen inganta narkewar abinci , tana kara ruwa a jiki, sannan kuma tana taimakawa masu ciwon sukari da kuma kare zuciya.
Abubuwan hadawa
- Kubewa
- Kifi
- Nama
- Kayan miya
Yadda ake hadawa
Dan samu a kada miyar kubewa danya mai dandano na dadi, a bi wadannan matakai masu sauki.
- Ki gurza kubewarki, ki daka a turmi tare da ‘yar kanwa.
- Ki gyara kifinki, ki sa a tukunya.
- Ki yanka albasa da kayan kamshi ya dahu sosai.
- Sai ki sa manja ki kara ruwa kadan saiki sa maggi da gishiri kadan
- Idan ya tafasa sai ki zuba kubewar Ki barta ta dahu
- Za kiga tayi yauki da kyar ki ke debowa.
- A gefe guda kuma sai ki yi jar miya da nama ko kaza sai ki zuba jar miyar a gefen miyar kubewar.
Za ku iya duba yadda ake miyar vegetable soup da kuma yadda ake miyar kuka da makamantansu.
A ci dadi lafiya.





