Skip to content

Yadda ake masa

Share |
Yadda ake masa
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Uwargida ga yadda ake masa cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi shida ne da steps hudu kacal.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa kofi 2 (shinkafan tuwo)
  2. Yeast cokali 2 (ki tabbatar mai kyau ne)
  3. Baking powder cokali 1
  4. Dafaffen shinkafa (ya dahu sosai) 1/3 kofi
  5. Sugar
  6. Man gyada

Yadda ake hadawa

  1. Da farko dai za ki wanke shinkafarki, ki jikata da safe, da yamma a kai markade.
  2. Idan a ka kawo, sai ki juya ki zuba yeast da sugar da baking powder, ki juya sosai, sai ki rufe, ki sa a waje mai dumi. Zuwa safiya ya taso ya kumbura.
  3. Da safe ki watsa dafaffafiyar shinkafarki, ki juya, ki sa ruwa dan dai dai ya yi kauri (amma ba sosai ba).
  4. Sai ki dauko kaskon tuyar masarki ki sa man gyada ya yi zafi, sai ki rika zuba kullinki kadan-kadan, idan kasan ya yi sai ki juya dayan gefen, idan ya soyu ki kwashe, haka za ki ta yi har ki gama. Ana iya cin masa haka ko kuma aci da miyan taushe ko stew ko sauce da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

Karin bayani

Za ki iya yanka albasa kanana a cikin kullin , sannan ki jajjaga attarugu ki zuba a cikin kullin .

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Yadda ake masa”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×