‘yan uwa mu koyi yadda ake beetroot smoothie cikin sauki, abubuwan hadawa guda hudu kacal, matakai guda uku kawai.
Abubuwan hadawa
- Mangoro
- Suga
- Beetroot
- Ruwan kankara
Yadda ake hadawa
- Ki nika mangoro da suga ki sa ruwan kankara ya hade ko ina sai ki raba gida biyu ki ajiye a gefe.
- Ki samo beetroot ki nika, ki tace ruwan sa sai ki hada da rabin juice din magoron sai ya baki wannan kala kamar ruwan goro.
- Sai ki samo kofinki wanda za ki zuba a ciki sai ki zuba daya juice din rabi sai ki dauko dayan ki na zubawa ta saman dayan a hankali da cokali.
Hikiman a zubawan ana so kada kala biyun su hade ne.