Skip to content

Yadda ake local jollof rice

yadda ake local jollof rice
5
(1)

Ku koyi yadda ake local jollof rice ga dadi ga kuma kyau. Wannan hadin jollof rice din gangariya ne dan gargajiya mai dauke da salon zamani.

Abubuwan hadawa

  1. Tafashashshe shinkafa
  2. Manja
  3. Tarugu (ki jajjaga)
  4. Daddawa (ki daka)
  5. Cray fish
  6. Albasa (ki yanka)
  7. Tumatur (ki yanka)
  8. Kabeji (ki yanka ki wanke da vinegar)
  9. Maggi
  10. Kayan kamshi
  11. Albasa
  12. Ganyen curry
  13. Soyayyen kifi

Yadda ake hadawa

  1. Dauko tukunya ki sa akan wuta ki sa manja ki yanka albasa ki kawo tarugu (ki jajjaga) da garin daddawa ki sa ki soya sama sama.
  2. Sannan kawo kayan kamshi, da maggi iya dandanon da zai mi ki sai ki tsaida ruwa (iya wanda zai kara dafa miki shinkafan ki).
  3. Sannan ki rufe nadan wani lokaci idan ya tafasa dauko shinkafan ki sa ki juya sannan kawo cray fish ki sa da ganyen curry, ki sa ki juya a hankali. Ki rife tukunyarki har sai ya nuna sai ki sauke ki sa a plate ki kawo albasa da tumatur, da kuma kabeji da soyayyen kifinki ki sa a gefe.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×