Skip to content

Yadda ake hadin fanke na musamman

fanke
0
(0)

Fanke wato puff-puff a turance abinci ne mai sauƙin yi kuma mai daɗi, wanda ake so sosai a ƙasashen Afirka, musamman a Najeriya da Ghana. Ana yin sa ne da garin fulawa, sukari, da yisti, sannan a soya shi a man gyada mai zafi. Yana da laushi a ciki kuma yana da ɗan ƙwari wato crispy- crispy a wajen ta.

Asali ma fanke ana yawanci sa ne a matsayin abincin karin kumallo wato breakfast idan an hada ta da shayi, koko, ko kunun gyada ko kunun tsamiya da dai makamantan su. Fanke ana iya cin ta a matsayin abin ciye-ciye wato small-chops ko a gida ko wajen taron bukukuwa ko walima.

Abubuwan hadawa 

  • Flour
  • Yeast/Baking powder
  • Suga
  • Kwai
  • Madarar gari

Yadda ake hadawa

Abi wadannan matakai masu sauki domin samun fanke mai dadi da danko.

  1. Ki tankade  flour irin ta Dangote bread flour, ki zuba a kwano.
  2. Ki sa zuba yeast dinki da sugar a dan kwano ki zuba ruwa dumi kadan ki bar shi na minti 5 haka, zaki ga ya dan yi bubbles haka. Hakan yana nuna cewa yayi proofing kenan.
  3. Sannan ki zuba baking powder da madarar garin ki a cikin flour din da kika tankade.
  4. Ki zuba sugar dinki da kwai da kika kada , sai ki kawo yeast dinki da kikayi proofing ki dama da ruwan dimi.
  5. Kada ki cika ruwa kuma kada ki yi kwauron ruwa.
  6. Ki buga sosai ki saka a rana ko guri mai dimi ki barshi kamar minti 30 zuwa 1 hour.
  7. Sai ki dora man ki, ki yanka dan albasa a ciki sai ki bari yayi zafi. Idan albasan ki ya fara kamshi, sai ki fara squeezing kullin fanken a cikin mai. In ya yi za ki ga ya yi brown, shi ke nan sai a kwashe. Haka za ki ta maimaitawa har ki gama.
  8. Bayan kin kwashe fanke, zaki iya cin sa da  kunun tsamiya, kunun gyada  ko da bakin shayi, ko dai da duk abinda ki ke so. Sanan zaki iya glazing dinsa da chocolate syrup, ko white chocolate syrup wato glazed puff puff, ko ki barbada garin madara akai dan kawata shi. Zaki ya dan garnishing dinsa ma da salan strawberries idan kina so.

Aci lafiya!

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×