Ku koyi yadda ake hada spicy pancakes and potato fillings. Wannan recipe ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya!
Abubuwan hadawa
- Filawa
- Tarugu
- Albasa
- Dankali (Irish)
- Maggi
- Seasoning
- Kwai
- Man gyada
- Baking powder
Yadda ake hadawa
- Farko za ki zuba flour da baking powder a bowl ki kwaba su da ruwa kar ya yi kauri sossai.
- Ki fasa kwai ki sa da maggi da sauran seasoning da curry da tarugu da albasa amma yankan ya zama kanana.
- Ki dora non stick pan akan wuta idan ya yi zafi ki na zubawa har ya yi brown ki juya.
- Idan kin gama sai ki zuba soyayyen dankali a ciki ki rufe kaman tabarma. Za a iya ci da cabbage sauce ko wani sauce na daban ko dai duk abinda ya yi wa mutum.