A yau zan gabatar da yadda ake hada potatoe balls, in ba a manta ba a baya munyi bayani akan yadda za ki hada shredded chicken sauce da wadansu miyoyi na zamani.
Abubuwan hadawa
- Potatoes (irish)
- Tarugu
- Albasa
- Seasoning
- Man gyada
- Kwai
- Flour
Yadda ake hadawa
- Farko za ki dafa dankali har ya dahu sai ki bari ya huce sannan ki yi mashing dinshi ki kwashe.
- Ki daka tarugu da albasa ki zuba ki saka spices dinki da seasoning.
- Ki saka lawashi sai ki juya ko ina ya hade. Ki dinga diban wanann mixture ki na making balls a hannun ki ki na ajiyewa.
- Ki barbada masu flour. Za ki kada kwai ki sa mishi salt, ki daura pot ki zuba oil idan ya yi zafi ki na dipping balls cikin mai ki na soyawa. A ci lafiya
Sannan za a iya: Yadda ake hada pakijis (egg bondas) da yadda ake hada vegetable rice da sauransu.