A yau kuma zamu duba yadda ake hada pepper soup na kifi ba tare da ya watse ba, ba kuma za ki ji qarnin shi ba ko kadan.
Abubuwan hadawa
- Kifi
- Lemun tsami
- Tattasai
- Tarugu
- Albasa
- Lawashi
- Seasoning da maggi
- Garlic
- Kayan kamshi
- Fish spices
Yadda ake hadawa
- Farko za ki wanke kifin tsaf sannan ki tsane shi ki sake wankewa idan kina da vinegar ki diga ki sake sa lemun tsami.
- Ki sa shi a tukunya ki sa ruwa kadan kaman 1/2 kofi ki dora a wuta.
- Ki zuba garlic da seasoning da komai a lokacin.
- Idan ya fara dahuwa ki sa albasa da lawashinki a ciki.
- Kada ki juya shi tururin Saman ya ishi saman kifi baya da wuyar dahuwa.
- Idan ya dahu sai ki sauke. A ci lafiya
Wannan shine yadda ake hada pepper soup na kifi. Na gode. sai mun hadu a girkinmu na gaba. Amma kafinnan za a iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake vegetable egg sauce da yadda ake chocolate cake.