Ku koyi yadda ake hada Nigerian lettuce salad. Wannan salad ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!
Abubuwan hadawa
- Lettuce
- Bama
- Albasa
- Tattasai
- Tumatir
- Gishiri
- Cucumber
- Vinegar
- Paprika
Yadda ake hadawa
- Farko za ki wanke lettuce ki yanka shi kanana sosai ki sake wanke shi tare da ruwan vinegar.
- Ki yanka sauran kayan baki daya slices kanana ki zuba.
- Ki hade su tare ki sa paprika tare da bama da gishiri. Shi ke nan an gama. Za a iya cin wannan salad da duk abunda ake so.