A yau zamu koyi yadda ake hada Nigerian jollof rice mai nagarta da dadi. Wannan shinkafar ta hadu, ku biyo ni ku sha labari!
Abubuwan hadawa
- Man gyada
- Tarugu
- Tumatur
- Tattasai
- Albasa
- Maggi
- Spices da seasoning
- Peas
- Carrots
- Kifi
Yadda ake hadawa
- Farko za ki zuba mai a cikin pot ki sa albasa, ki zuba tattasai da tarugu da tumatur da ki ka hada ki ka markada. Sai ki juya ki tsayar da ruwan dahuwar shinkafarki. Ki zuba seasoning da spices.
- Sai ki saka shinkafa, idan ya kusan kare dahuwa sai ki saka peas, carrots. Ki juya ta idan kina bukatar busashen kifi sai ki zuba a ciki kafin ta tsane. A juya a sauke.
Za a iya duba: Yadda ake dambun shinkafa mai gyada da yadda ake dambun nama da sauransu.