Ga kuma yadda ake hada miyar sure (yakuwa). wannan miyar nata salon na musamman ne.
Abubuwan hadawa
- Ganyen sure
- Tattasai da tarugu
- Albasa
- Maggi da spices
- Daddawa
- Kuli-kuli
- Manja
- Nama
- Tafarnuwa
Yadda ake hadawa
- Farko zaki tafasa namar ki a cikin tukunya, sai ki sauke ki zuba shi a cikin bowl.
- Ki saka manja a cikin tukunyarki sannan ki saka albasa. Idan ya fara soyuwa sai ki saka tafasashen namarki a ciki tare da tattasai da tarugu da aka nika.
- Ki dan soya su na mintuna sai ki zuba ruwa tafashen ki a ciki. Ki kara kufi 2 na ruwa ki saka maggi da tafarnuwa da daddawa da sauran kayan kamshi da kike da a ciki ki rufe.
- Sai ki yanka sure da albasa ki ajiye a gefe, idan ruwan miyan suka tafasa sai ki saka, bayan kaman minti 5 sai ki saka kuli-kulii ki juya. Za kiga ya yi kauri sai a sauke aci da tuwon shinkafa.
Kuna iya duba miyar yakuwa, da yadda ake miyar kubewa mai ugu da sauransu.
Photo credit: Fatima Babagana