A yau zamu koya yadda ake hada fluffy beans cake (alale).
Abubuwan hadawa
- Wake
- Crayfish
- Koren tattasai
- Tarugu
- Tattasai
- Seasoning
- Manja
- Lawashi
- Albasa
Yadda ake hadawa
- Farkon za ki debi wake ki tsince datti ki surfa shi ki gyara, sai ki zuba ruwa da garlic a ciki ki markada ki yanka koren tattasai a ciki da lawashi da albasa.
- Ki grating tarugu da tattasai ki zuba, ki sa manja, da seasoning da cray fish ki sa whisk ki juya shi sosai.
- Ki shafa mai a jikin moi moi containers dinki sai ki dinga zuba kullunki a ciki.
- Ki dora ruwa dai dai yadda ba za su rufe containers ba, idan sun tafasa ki jera containers a ciki ki rufe.
- Idan ya dahu ki sauke, za a iya ci da cabbage sauce da muka yi a baya, za kuma a iya duba fish egg sauce ko wani sauce makamantansu.