Juice na carrot na daya daga cikin nau’ikan lemu da ke da matukar amfani ga biladama. Uwargida ga dama na koyon yadda za ki saffara carrot cikin mintuna kalilan ki samu ingantaccen carrot juice. Bismillah!
Abubuwan hadawa
- Karas
- Sugar
- Lemun tsami
- Flavour
- Lemun zaki
Yada ake hadawa
- Farko za ki wanke karas ki yi peeling bayan ki yanka kanana.
- Ki saka shi cikin blender ki nika. Ki yanka lemu duka ki matse ruwan wuri daya.
- Ki tace ruwan lemun da na karas ki hade wuri daya. Ki sa sugar da flavour, sannan ki sa kankara. Sai a sha.
Za a iya duba: Cucumber and mango juice da yadda ake hada nigerian lettuce salad da sauransu.