Skip to content

Yadda ake hada bitter leaf soup

Share |
yadda ake hada bitter leaf soup
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

A yau zamu duba yadda ake hada bitter leaf soup, miya ce mai dadi a baki,ga magani, ba sai na tuna muku amfanin shuwaka wurin gyara ciki ba.

Abubuwan hadawa

  1. Manja
  2. Nama
  3. Seasoning
  4. Garlic 
  5. Ginger
  6. Shuwaka (bitter leaf)
  7. Tattasai
  8. Tarugu
  9. Albasa

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki yanka nama ki sa ruwa a ciki ki yanka albasa ki dora shi akan wuta.
  2. Sai ki yanka shuwaka dinki itama ki zuba ta a cikin tukunya ki tafasa ta (amfanin wannan zai cire maki dacin shuwaka har yara su iya cin ta su ma).
  3. Sai ki zuba wannan shuwaka a cikin blender ki yanka albasa mai yawa ki nika su a tare, ki aje gefe dan ci gaba da hada miyarki.
  4. Ki zuba nikakken tattasai da tarugu a cikin ruwan naman ki dake tafasa sai ki juya, ki saka manja ki rufe.
  5. Bayan mintina biyu sai ki sake budewa ki juya ki saka seasoning da garlic and ginger na ki a ciki, Ki dauko nikakken shuwaka da albasa da ki ka hada ki zuba a ciki ki juya.
  6. Ki rufe ya dahu, sannan ki dandana ko da bukatar karin gishiri a miyar ki. Za ki iya cin wannan miyar da ko wane irin tuwo. Aci lafiya.

Zaku iya duba wasu miyoyinmu da muka yi a baya, kamar su Miyar hanta, miyar sure (yakuwa) da sauransu.

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading