Skip to content

Yadda ake fried rice

Share |
yadda ake fried rice
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake fried rice mai dadi ga kuma kyau. Wannan fried rice ne da idan kun taba sai kun manta inda ku ke. A gawada mu ji labari.

Abubuwan hadawa

 1. Shinkafa
 2. Kayan lambu (karas,koriyar wake, peas, sweetcorn)
 3. Tumeric powder (kurkur me hade da kayan Kamshi)
 4. Man gyada
 5. Maggi chicken na star
 6. Thyme
 7. Albasa
 8. Jajjagen tarugu

Yadda ake hadawa

 1. Da farko ki wanke shinkafa, ki tsane ruwansa kaf, sai ki daura mai a tukunya ki zuba shinkafa a ciki.
 2. Ki yi ta juyawa har shinkafan ya soyu,sai ki kawo kayan lambu ki saka, sannan ki sa tumeric da thyme da maggi, ki saita ruwan da zata dafa shinkafar, sai ki rufe.
 3. Sai shinkafar ta dauko dahuwa sai ki kawo kayan lambu da albasa da jajjagenki, ki zuba ki gauraya ki rufe, ki bari har ya tsotse ruwan tsaf ya dahu.

Wannan shinkafar ta na da dadi sossai musamman aka hada ta da soyayyiya ko gasashshiyar kaza.

Sannan a kwai hanyoyon yinta da yawa, da sannu a hankali in kuna binmu a Bakandamiya za mu kawo mu ku su ba da jimawaba insha Allah. Mun gode, sannan za a iya duba: Yadda ake sandwich da Oreo milkshake da sauransu.

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading