Ku koyi yadda ake sandwich ga dadi ga kuma kyau. Wannan sandwich na da saukin gaske wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Bredi mai yanka yanka
- Kwai dafaffe
- Mayonnaise
- Kifin gwangwani
- Maggi da dan chili sauce
- Mozzarella cheese (jubnar mozzarella)
Yadda ake hadawa
- Ki yayyanka kwai ki sa kifin gwangwani da mayonnaise da maggi da dan chili sauce ki hade su wuri daya.
- Sai ki dauko biredi guwa uku ki cire gefensu, sai ki ajiye daya ki shafe da hadin da ki ka yi na su kwai da kifi sai ki sa wani biredin sai ki kawo jubnar mozzarella ki shimfida sanna ki kawo wani biredin ki rufa, sai ki sa wuka ki raba su ta tsakiya. Haka za ki yi ta yi har biredinki ya kare.
‘Yan uwa a ci dadi lafiya, sai kun jimu wani makon. Sannan za a iya duba: Cream caramel da oreo milkshake da sauransu.