Skip to content

Yadda ake doya mai kwai

Share
yadda ake doya mai kwai
0
(0)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Bansan wanda ba ya son doya da kwai ba,amma kuma ba kowa ne ya iya hadawa ba. Saboda haka yau mun kawo muku yadda ake doya da kwai cikin sauki.

Abubuwan hadawa

  1. Doya
  2. Kwai
  3. Maggi
  4. Tarugu
  5. Man gyada
  6. Albasa da lawashi

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki yanka doya ki tafasa ta ki sa gishiri kadan sai ki zuba wannan doya a bowl.
  2. Ki samu wani bowl ki fasa kwai ki sa tarugu, da maggi, da albasa ki kada shi.
  3. Ki dora mai a cikin frying pan. Idan ya dauki zafi ki rika tsoma doyan a ruwan kwan, sannan ki rika tsomawa cikin man gyadan.
  4. Ki juya gefe dayan idan ya yi, sai ki kwashe idan shima gefen ya yi.

Za a iya dubaYadda ake shredded chicken sauce da yadda ake dambun nama da sauransu.

How many stars will you give this recipe?

1 thought on “Yadda ake doya mai kwai”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page