Skip to content

Yadda ake desiccated coconut balls

Share |
Yadda ake hada desiccated coconut balls
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Yadda ake desiccated coconut balls, Uwargida ga kayan da ba a baiwa yaro mai kwuya, desiccated coconut balls, dadi iya dadi. Ga yadda ake sarrafawa a kasa kamar haka.

Abubuwan hadawa

  1. Desiccated coconut (raba kashi biyu)
  2. Condensed milk
  3. Butter 1 tblspn

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki nemi desiccated coconut ne sai ki raba shi biyu, domin a karshe za ki sake bukatar shi, ki samu pan mai dan zurfi ki saka butter dan kadan a cikin pan din har ya yi melting.
  2. Idan ya narke sai ki zuba desiccated coconut a ciki ki rage wuta ki dinga juya shi a hankali kaman mintina biyar za ki ga ya fara laushi sai ki zuba condensed milk a ciki ki ci gaba da juyawa a hankali har ya hade jikin shi.
  3. Idan ya hade jikinshi ki sauke shi ki dinga diba kina yin balls a hannunki, sai ki saka cikin waccan desiccated coconut da ki ka diba gefe har ko ina ya ji. Haka za ki yi har ki gama. Za ki iya garnishing da chocolate kaman irin su Nutella haka. A ci lafiya.

Mai karatu na iya duba: Yadda ake hada ring chocolate cookies da yadda ake hada coconut pound cake da sauransu

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×