Skip to content

Yadda ake dambun shinkafa na musamman

Share |
Yadda ake hada dambun shinkafa
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Uwargida ki shirya tsaf dan koyan yadda ake dambun shinkafa na musamman.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Zogale
  3. Nama
  4. Albasa mai ganye
  5. Mangyada
  6. Kayan miya
  7. Maggi
  8. Kori (Curry)
  9. Gishiri
  10. Cittah da tafarnuwa

Yadda ake hadawa

  1. Ki gyara shinkafarki ki wanketa ki tsane
  2. A barzo miki shi a inji sai ki ajiye a gefe
  3. Sai ki wanke namanki kidora awuta. Ki sa maggi, da  gishiri, da tafarnuwa, da citta, da albasa
  4. A gefe guda kuma ki tankade barzazzen shinkafarki, domin da tsakin za ki yi amfani
  5. Sai ki sa ruwa ki wanke tsakin ki tsane shi, sai ki zuba shi a madambaci ki dora a wuta.
  6. Sai kuma ki gyara zogalenki, ki wanke, ki hada da tsakin sai ki rufe.
  7. Ki tsame namanki, sai ki yanka kayan miyanki ki ajiye a gefe.
  8. Uwargida sai ki duba tsakinki idan yayi za ki ji yana kamshi kuma tsakin ya dahu
  9. Sai ki sauke ki zuba a roba mai fadi, sai ki zuba soyayyen manki, da albasa, da sauran kayan miya: maggi, da gishiri, da kori, da tafarnuwa, kuma ki juya ki daddanna sosai sai kin fahimci komai ya yi dai-dai
  10. Sai ki zuba dan ruwan tafasashen naman ki juye atukunya ki maida shi wuta ki bashi kamar minti sha biyar, za ki ji gida yadau kamshin girkinki.

Mai gida na shigowa, hhmmn…, sai san barka da godiya.

Photo Credit: Esha’s Kich

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×