Dambun nama dai kusan in ce kowa ya san shi kuma kuwa na so to amma ba kowa ne ya iya yadda ake sarrafa shi ba. Ga yadda ake dambun nama dalla dalla na kawo mana. Uwargida biyo ni ki sha labari!
Abubuwan hadawa
- Nama/kaza
- Tarugu
- Albasa
- Tafarnuwa
- Seasoning
- Maggi
- Man gyada
Yadda ake hadawa
- Farko za ki wanke nama ko kaza ki zuba cikin tukunya ki zuba albasa da tarugu da tafarnuwa.
- Ki dora a wuta, ki barshi ya yi ta dahuwa kaman awa 4/5 yana dahuwa.
- Idan kin sauke, sai ki raba shi da kashi da kitsensa ko fata duka ki cire ki mayar da tsokar ki sa muciya ki tuke shi ki sa seasoning da spices.
- Sai ki zuba man gyada har ya rufe naman ki soya. Ba za ki daga ba ki na yi kina juya shi har ya yi.
- Sai a kwashe a saka a cikin abun tata a matse man. A tabbar ba sauran mai sai a zuba cikin sieve ko colander. A ci lafiya
Za a iya duba: Yadda ake mixed fruit juice da yadda ake hada sweet pancakes da sauransu.
Photo credit:Wiki Hausa