Skip to content

Yadda ake dambun kaza

Dambun kaza
0
(0)

Dambun kaza wani shahararren abinci ne na gargajiya a ƙasar Hausa, wanda ake yi da naman kaza kamar yanda ake dambun naman da ake yi da da naman sa. Ana yin shi ne ta hanyar dafa naman kazan har sai yayi laushi tare da su kayan dandano.

Bayan naman kazan ya dahu yayi laushi, ana yayyaga naman, ko a murƙushe, ko a nika shi a inji dan ya zama ƙanana-ƙanana. Daga nan sai a soya shi da mai kaɗan tare da kayan ƙamshi da danadano kamar su barkono da albasa,curry da thyme harda ma tafarnuwa har sai ya bushe yayi laushi kamar audiga.

Ita dambun kaza ana yawan cin sa a lokutan bukukuwa irin su bikin sallah, bikin suna, bikin aure harda ma biki. Dambun kaza yana da sauƙin hadawa yayin da ana iya cin shi tare da abubuwa kamar kunu, fura, ko kuma a ci shi kaɗai a matsayin abin ciye-ciye kuma yana iya ɗorewa na wasu kwanaki ba tare da ya lalace ba. Ita dai naman kaza tana daga cikin abincin da ke nuna al’adun Hausawa da ƙwarewarsu wajen sarrafa nama.

Abubuwan hadawa

  • kaza
  • Man gyada
  • Attarugu
  • Albasa
  • Dandano
  • Tafarnuwa(idan ana bukata)

Yadda ake hadawa

Domin sarrafa nama don samun dambun kaza, abi wadannan matakan masu sauki.

  1. Dafarko uwargida zata tanadi kazarta mai kyau mai tsabta sai ta wanketa sosai ta dora a wuta tare da albasa da tafarnuwa, ki barta ta dahu sosai tayi luguf.
  2. Idan ta dahu sai ki sauke, ki cire duk kashin dake jiki tare da duk wani kitse, bayan kin gama cirewa sai ki zuba ta a turmi.
  3. Bayan kin jajjaga attarugunki sai kiyi ta daka kazar har sai tayi laushi.
  4. Daga nan sai ki zuba dakakkiyar kazar a tukunya ko kaskon suyarki, ki zuba kayan kamshi da dandano, sannan ki zuba mai.
  5. Sai ki yi ta juyawa, kina juyawa kina kara mai har sai kinga ya soyu, sai ki sauke. Shikenan kin gama sarrafa dambun kazan ki.

A ci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×