Skip to content

Yadda ake chocolate buns

yadda ake chocolate buns
5
(3)

Ga yadda ake chocolate buns masoya girkin Bakandamiya Kitchen. Ku biyo mu ga yadda ake yi dalla dalla.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 2
  2. Baking powder cokali karami 2 (tspn)
  3. Butter cokali babba 2  (tbsp)
  4. Sugar cokali babba 3
  5. Gishiri kadan
  6. Madara ¼ kofi
  7. Nutmeg ½ cokali
  8. Ruwa ½ kofi
  9. Chocolate (irin na kanana ma leda yan naira 40-50)

Yadda ake hadawa

  1. Ki tankade filawarki a kwano mai dan girma, sai ki zuba baking powder, nutmeg, madarar gari, gishiri sai ki juya.
  2. Dauko butter ki sa a cikin filawa ki murja har sai ya hade jikansa sai ki sa sugar, ki fasa kwanki a ciki da ruwa ki kwaba shi ya kwabu sosai sai ki ajiye a gefe na dan wani lokacin kamar minti 15-20.
  3. Daura man gyada akan wuta idan ya yi zafi sai ki dauko chocolate na ki ki na sawa a kwabin filawa kina kamar mulmula shi kina soyawa a mai har sai ya soyu (karki cika masa wuta don kar ya miki tuwo a ciki) sai ki tsane a matsani. A ci dadi lafiya.

Mai karatu wannan shine yadda ake chocolate buns. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba. Amma kafin nan, mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: yadda ake egg roll shawarma da kuma yadda ake potato balls da makamantansu.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×