Skip to content

Yadda ake egg roll shawarma

Share |
Yadda ake egg roll shawarma
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake egg roll shawarma cikin sauki, abubuwan hadawa guda sha biyu, matakai guda goma takwas.

Abubuwan hadawa

  1. Kwai
  2. Shawarma bread
  3. Naman shanu Ko kaza (dafaffafe, ki yanka kanana)
  4. Tarugu
  5. Albasa
  6. Maggi
  7. Kabeji (ki yanka ki wanke da gishiri)
  8. Tumatur
  9. Tomato ketchup
  10. Koren tattasai
  11. Cucumber
  12. Karas (carrot)

Yadda ake hadawa

  1. Ki gyara, ki wanke sai ki yanka su carrot na ki, kabeji, albasa ajiye a gefe.
  2. Ki sa non stick pan na ki akan wuta ki sa butter kadan (cokali daya), sai ki sa yanka albasa ki dan soya sama sama, ki sa tarugu ki juya , sai ki sa ruwa kamar (cokali biyu).
  3. Sai ki kawo namanki tare da kayan kamshi, maggi (iya dandano da zai mi ki) sai ki juya ki rufe nadan wani lokaci sai ki kawo kabejin, cucumber da ki ka yanka ki sa a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye ki sauke ki ajiye a gefe.
  4. Ki dauko wani kwano daban ki fasa kwanki a ciki sai ki sa gishiri kadan, ki yanka albasa ki yanka tarugu ki sa a ciki sai ki buga ajiye a gefe.
  5. Ki sake daura non stick pan ki sa man gyada kadan sai ki dauko hadin kwanki (wanda ki ka yanka albasa da tarugu a ciki) ki zuba dan dai dai a cikin non stick pan na ki (wanda ki ka sa man gyada) sai ki dauko shawarma bread naki ki daura akan kwan dake kan wutan.
  6. Sai ki dauko cokali ko kuma ki sa hannunki ki na danna shi a hankali har sai Kwan da shawarma bread din sun hade da juna. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran.
  7. Sai ki dauko ki daura a kan plate ko tire ki dauko hadin kabejinki ki sa akan shawarma bread din (wanda ki ka manne shi da kwai) sai ki dauko su koren tattasai albasa da carrot na ki ki sa a gefe (idan ki na so za ki iya sa tomato ketchup, salad cream naki a wannan mataki).
  8. Sai ki masa nadin tabarma (za ki iya sa foil paper bayan kin gama nadawa don kar ya ware). A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×