Skip to content

Yadda ake boiled egg sauce

Yadda ake boiled egg sauce
4
(4)

Ku koyi yadda ake boiled egg sauce mai kyau da kuma inganci. Makatai hudu kacal uwargida za ta bi ta kammala wannan kayataccen sauce.

Abubuwan hadawa

  1. Kwai (dafaffafen kwai)
  2. Kayan ciki
  3. Tumatur (ki yanka)
  4. Kayan kamshi (ki yanka kanana)
  5. Tarugu (jajjaga)
  6. Maggi
  7. Lawashi (wanke a yanka)
  8. Albasa (a yanka)
  9. Man gyada

Yadda ake hadawa 

  1. Dauko kwanki ki yanka kanana dai dai, Kayan ciki ki yanka kanana a jiye ko wanne a gefe.
  2. Daura tukunya akan wuta ki sa man gyada kadan ki yanka albasa ki soya sama sama, ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama shima.
  3. Sai ki dauko Kayan ciki ki sa, ki kara ruwa kadan ki sa a ciki, dauko Kayan kamshi ki sa, maggi ki sa iya dandano da zai miki ki juya rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan har sai ruwan ya dan shanye.
  4. Sai ki dauko tumatur ki sa ki kawo kwanki, lawashi ki sa ki juya a hankali ki rufe nadan wani lokaci, sai ki sauke. A ci dadi lafiya

Ana iya cin boiled egg sauce da alale ko dahuwar farar shinkafa ko couscous ko ma dai taliya da makamantansu. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×