Skip to content

Yadda ake banana and coconut ice cream

Share |
Yadda ake banana and coconut ice cream
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake banana and coconut ice cream cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi bakwai ne da steps uku.

Abubuwan hadawa

 1. Ayaba
 2. Madarar kwakwa
 3. Madara
 4. Sugar
 5. Flavour
 6. kwakwa (ki gurza)
 7. Chocolate

Yadda ake hadawa

 1. Ki dauko ayaban ki bare ki yanka ta kanana ki sa a blender ki kawo madarar kwakwa, da madara (ta ruwa) ki sa ki zuba sugar iya yanda ki ke son zakin ya kasance.
 2. Sai ki markada ya markadu sosai sannan ki juye a roba ki sa a freezer ya yi kankara. Sai a sami cokali mai zurfi ki na diba ki na sawa a kofi, sannanki sa wani karamin kwano.
 3. Daga karshe ki yaryada chocolate a kai da gurjajjiyar kwakwa shima a kai. A sha dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Yadda ake banana and coconut ice cream”

  1. Madarar kwakwa shine coconut milk. Ana sayarwa a kasuwa ko kuma za ki iya yi a gida. Yadda za ki yi a gida shine, ki samu kwakwarki ki cire bayan ki bar wannan farin kawai. Sai ki markada a blender, ki sa ruwa ki tace idan ya markadu, wannan ruwan shine madarar kwakwa.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading