Awarar waken soya wato Awara, abinci ne da ake samu daga waken soya. Yana da matuƙar amfani ga lafiyar jiki saboda yalwar sinadarin furotin da yake ɗauke da shi. A yawancin yankunan Arewacin Najeriya, awara yana daga cikin abincin da jama’a ke so sosai; ana cin sa da gurasa, koko, ko kuma a soya shi domin jin daɗi a matsayin abincin marmari. Awarar waken soya yana da sauƙin samu da hadawa ga kuma arha, hakan ya sa ya zama abinci mai muhimmanci a kasar Hausa.
;Abubuwan hadawa
- Waken soya
- Attarugu
- Albasa
- Ruwan tsami ko dan tsami
- Dandano
Yadda ake hadawa
Abi wadannan matakai masu sauki don hada hadadden awarar waken soya mai dadi.
- Da farko zaki wanke waken soya sosai domin cire ƙura da datti.
- Bayan nan sai ki jika waken soyan a ruwa na tsawon awa 6–8 ko ki bar shi ya kwana dare ɗaya domin ya yi laushi.Sai ki sake wanke shi sannan ki kai a markado miki ko ki marakada abinki a gida idan kina da engine markada wato blender irin su Buchymix blender.
- Idan an kawo daga markade sai ki dan diga manja aciki, ki dan kara ruwa saiki tace.
- Idan kin gama ki zuba a tukunya ki dora a wuta.
- Sai ki dauko attarugunki ki jajjaga ki yanka albasa.
- Ki dinga kula da wannan ruwan awararda ki da kika dora. Idan ya fara tafasa saiki dauko ruwan tsaminki ki zuba a ciki, za kiga duk ta hade jikinta
- Sai ki zuba albasa da attarugu da dandano aciki, idan ta dan kuma dahuwa saiki samu abin tata ki juye awaran a ciki ki daure shi sosai ki samu abu mai nauyi ki danne ta ko kuwa ki rataye yadda ruwan zai dige daga jikin awaran.
- Idan kin tabbatar ruwan ya gama digewa kuma ya huce, sai ki yanka shi ƙanana-ƙanana ko dai-dai yanda kike so.
- Bayan nan sai ki daura mai ki bari yayi zafi sannan ki fara soyawa har sai ya yi golden brown. Shikenan awararki ta hadu.
- Zaki iya cin sa da kunun tsamiya, ko lemon kankana mai sanyi.
Atakaice dai Awarar waken soya wacce aka sani da tofu a wasu sassan duniya, abinci ne mai saukin hadawa da kuma matukar amfani wajen gina lafiyar jiki. Aci dadi lafiya.





