Ku koyi yadda ake suyan dankali mai nama da kwai. Wannan hadin dankali mai nama da kwai yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Dankalin (irish)
- Nama mai kyau 1/3 kilo
- Kwai 4
- Gishiri
- Man gyada
- Tsinken tsokale Hakori (toothpick)
Yadda ake hadawa
- Da farko ki fere dankalinki ki yanka a kwance sai ki wanke ki zuba a tukunya ki dora a wuta ki sa gishiri.
- Idan ya yi sai ki sauke, ki dauko namanki ki wanke ki tafasa da maggi, idan ya yi sai ki soya sama sama ki ajiye gefe.
- Sai ki dauko tsinken tsokale hakorinki, ki sa dankali daya da nama daya, a haka za ki yi ta jera su har sai kin kare.
- Sai ki fasa kwai a roba ki kada sosai ki sa manki a wuta, sannan ki dauko wannan dankalin ki na sawa a kwai, ki soya, idan ya yi sai a yi abin karyawa.
A ci dadi lafiya. Na gode.