Akwai hanyoyi da dama na yin fried rice. Tun daga kan coconut fried rice, vegetable fried rice, da sauransu. A yau na zo maku da wata hanya da za ki yi pineapple fried rice dinki mai dadi da sauki, sannan very unique.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups basmati rice
2- 2 big carrots
3- 3 tablespoons maggi powder
4- 1 tablespoon mixed spices
5- 1 cup vegetable oil
6- 1 and 1/2 cups pineapple juice
7- 1 teaspoon salt
8- 1 spring onion
9- 1 green bell pepper.
10- 1 tablespoon curry powder
Yadda ake yi
1- Ki zuba mai a cikin tukunta ko wok pan. Ki bar shi ya yi zafi. Sai ki kawo spices of your choice. Ni dai na yi amfani da bay leaf, paprika, ginger and garlic, rosemary, thyme, da oregano. Ki soya su saboda kamshin su ya fito sosai

2- Then ki kawo carrots dinki da kika yanka diced. Idan kina son wasu veggies din kamar green beans, peas, sweet corn duk sai ki hada ki zuba. Ni dai da carrots kawai na yi amfani

3- Sai ki zuba albasa da green pepper. Za ki iya saka yellow amd red peppers duka idan kina so.
4- Idan sun soyu kamshinsu yana fita. Sai ki kawo shinkafa wadda kika dafa 75% cooked. Ki dafa tare da salt

5- sai ki zuba seasoning
6- Sai ki saka curry wanda kike so (ducros is my all time favorite)

7- Sai ki saka chili flakes (yaji ne ake dakawa amma kada ya daku sosai)

8- Bayan kin motsa da kyau. Wannan ruwan abarba ne. Na markada na tace sannan na zuba a ciki. Za ki iya yanka abarbar into chunks ki soya su tare da veggies. Za ki iya yin kuma yadda na yi din nan

9- Sai ki rufe ruf, ki bari ta karasa dahuwa.

10- sai ki yi serving pineapple fired rice dinki

Za ku samu beautiful plates and trays a Bakandamiya shopping. Akwai su non stick pots da sauran nau’ukan kayan kitchen masu kyau.