Cake kala-kala ne, kuma hanyoyin sarrafa shi suna da yawa. A yau na kawo maku wani mai sauki, mai taushi, sannan mai dadi da kyau ko a ido.
Abubuwan Bukata:
1- 1 cup margarine
2- 3/4 cup sugar
3- 4 eggs
4- 3 tablespoons evaporated milk
5- 1 teaspoon flavor of choice
6- 2 cups flour
7- 1/4 teaspoon salt
8- 1/2 teaspoon baking powder
9- 2 tablespoons crushed oreos
10- 2 tablespoons crushed lotus biscuits
Yadda ake yi:
1- Za ki fara zuba sugar da margarine a cikin bowl sai ki mixing dinsu da handmixer ko kuma whisk har sai sun zama light and fluffy.

2- Sai ki dinga zuba kwai da kadan kina mixing.

3- ki zuba madara da flavor ki ci gaba da mixing dinsu.

4- Ki zuba dry ingredients dinki (flour, salt, and baking powder) sannan ki mixing har sai komai ya hade.

5- sai ki samu packs din da za ki a ciki. Ki zuba batter din sannan ki barbada oreos a sama.

6- Daga nan sai ki dauka ki kai a pre heated oven ki gasa a medium heat da wutar kasa kadai sai ta kusa gasuwa ki kunna ta sama.
