Uwargida ga yadda za ki hada dambun couscous da hanta ta hanyar bin matakai uku kacal. Ki gwada ki bamu labarin wannan hadadden recipe.
Abubuwan hadawa
- Man gyada
- Couscous
- Dafaffen zogale
- Tarugu
- Tattasai
- Koren tattasai
- Seasoning
- Albasa
- Lawashi
- Hanta
Yadda ake hadawa
- Farko uwargida zata dora ruwan zafi kadan idan ya tafasa sai ki yayyafa akan couscous ki rufe shi ki barshi ya dan turara.
- Ki wanke zogala, ki daka tarugu da tattasai ki yanka albasa sai ki zuba a cikin bowl, ki sa mai, koren tattasai, ki zube couscous dinki da ya turara. Sai ki saka seasoning yadda zai ji.
- Ki juya ko ina ya samu sai ki zuba a cikin tukunya ya turara mintina 5 kina juyawa dan kar ya kama. Sai ki sauke.
Yadda za ki yi hantar da za ki zuba
Ki wanke anta ki yanka albasa da yawa sai ki zuba su a cikin tukunya. Ki daka tarugu kaman biyu sai ki sa maggi ki barshi ya dahu za ki ga ya yi romo antar ta dahu sai ki zuba a sama. A ci lafiya.
Nice dambu😍i like it