Uwargida ki duba yadda za ki adana veggies na ki fresh tsawon lokaci. Idan kun bi wannan hanyar to kunyi bankwana da lalacewar veggies ke nan.
Ire-iren veggies da za a adana
- Koren wake
- Karas
- Masarar gwangwani
- Peas na gwangwani
- Lawashi
Yadda za a adana su
- Ki gyara koren waken ki, ki yanka shi irin yankan da ki ke so ajiye a jefe. Ki sa ruwa akan wuta idan ya yi zafi sai ki sa baking powder ko ruwan kanwa a ciki ki kashe wuta sai ki kawo koren wake ki sa a ciki ki barshi nadan wani lokaci kadan .
- Sai ki tace ki sake wanke shi da ruwa mai kyau ki sa a matsani ki tsane sa ki tabbatar ba ruwa a jikinsa. Ajiye a gefe.
- Dauko peas, da masarar gwangwani ki pape bakinsa ki zuba su a roba sai ki sheka masa shima ki tsane a matsani. Ki tabbatar ba ruwa a jikinsu. Ajiye a gefe.
- Dauko karas ki goge dattin bayansa ki yanka shi irin yanka da ki ke so ki wanke ki tsane sa a matsani. Ki tabbatar ba ruwa a jikin sa. Ajiye a gefe.
- Lawashi shima ki wanke ki yanka ki tsane a matsani.
- Daga karshe sai ki dauko duka veggies na ki ki hadasu gu daya sai ki sa a freezer ya yi kankara. Duke lokacin da ki ke da bukata sai ki fito da shi yadan sha iska kafin ki yi amfanin ki da shi.