Skip to content

Yadda ake vanilla cupcakes

Share |
Yadda ake vanilla cupcakes
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ga yadda ake vanilla cupcakes mu koya ‘yanuwa, recipe ne mai sauki da kuma dadi cikin ‘yan lokaci kadan uwargida za ki hada wannan cupcakes.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi biyu
  2. Kwai 7 ko 8 (yadanganta da irin girmansu)
  3. Butter 1 (shima leda 1)
  4. Baking powder karamin cokali biyu
  5. Filebo karamin cokali biyu
  6. Bushashahen inabi 7
  7. Suga kofi daya  (Ko ki zuba iya zakin da zai miki)
  8. Vinegar rabin kofi

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki tankade filawarki tare da baking powder,  sai ki ajiye a gefe.
  2. Ki sami mixer machine naki ki sa butterki a cikin wannan kwanon mixer (ko ki sami wani kwano daban idan da hand mixer za ki yi) ki yi ta motsashi na dan wani lokaci. 
  3. Ki kawo suga ki sa a ciki ki yita motsashi har sai suga ki ya narke a ciki (ba kijin gudajin sugar a cikin butter)
  4. Sai ki dauko kwai ki fasa ki yi ta motsashi (Kwan ana so ana sa shine daya bayan daya kuma ana motsashi bayan kowani sa kwai da akayi) har ki gama da kwanki. Sai ki dauko vanilla filebo ki sa ki motsa.
  5. Ki dauko filawanki da ki ka tankade tare da baking powder (zaki iya raba filawar gida hudu) ki rinka zubawa a hankali a cikin wannan hadin butter har ki gama da flour ki na motsashi.
  6. Bayan kin gama da mataki na 5 sai ki dauko vineger ki ki sa a ciki (amfanin vinegar shine yana sa cake yayi laushi ya kuma tashi),
  7. Ki dauko bushashshen inabinki ki zuba ciki ki motsa.
  8. Sai ki dauko abin gashin (nakan sa takakardar gashi a cikin abin gashin kafin na zuba kwalli cake nawa) ki zuba hadin Kwalli ki a cikin kowani takardar gashi ((ba’aso a cika shi don Kar ya zube a lokacin gashi ,ki sa su rabi rabi ko yadanfi rabi da kadan don ya yi gashi mai kyau)
  9. Sai ki sa a cikin magasa (prehated oven) ki gasa, har sai ya gasu (ko idan kinsa tsinke ya fito ba tare da komai ajikin sa ba) sai ki cire ki bari yasha iska. A ci dadi lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×