A yau za mu koyi yadda ake tuwon masara. Uwargida ki shirya tsaf dan koyon tuwon namu na musamman.
Abubuwan hadawa
- Garin masara
- Ruwa
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki dora ruwanki a wuta.
- Sai ki tankade garinki sai ki duba idan ruwan ya tafasa sai ki yi talge kibashi minti ashirin.
- Talge shine ki samu dan ruwan sanyi a wani kwano mai dan fadi, sannan sai ki zuba dan garinki kina juyawa har ya dan yi kauri kadan. Wannan shi za ki saka a cikin tafasasshen ruwanki ki bar shi kamar minti ashirin.
- Bayan talgenki ya tafasa sosai, sai ki dauko garinki kina zubawa kadan-kadan a cikin talgen kuma kina tukawa da sauri har sai tuwon yayi kauri yadda kike so.
- Sai ki rufe ki bashi kamar minti biyar sai ki sake tukawa ki kwashe ki malmala kisa a kwanonki mai kyau.
- Za a iya ci da miyar zogale ko kuka ko miyar kubewa mai ugu
Na gode.
Photo credit: Osomosemuaz