Skip to content

Yadda ake tasty beef wrap

Share |
Yadda ake tasty beef wrap
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake tasty beef wrap cikin sauki, abubuwan hadawa guda goma, matakai guda biyar kacal.

Abubuwan hadawa

 1. Dafaffafen naman (yanka 15 manya yanka amma)
 2. Shawarma bread (Uku)
 3. Carrot
 4. Kabeji
 5. Tumatur
 6. Albasa
 7. Maggi
 8. Kayan kamshi
 9. Butter
 10. Tarugu

Yadda ake hadawa

 1. Ki dauko dafaffafen naman ki yanka shi Kanana ko kuma ki yanka dogo dogo, sai ki ajiye a gefe.
 2. Ki yanka su kabejinki ki dan wanke da gishiri ki tsane a matsani, ki goge carrot na ki, ki yanka albasa, ki jajjaga tarugunki, sai ki ajiyeye a gefe
 3. Ki daura non stick pan naki akan wuta ki sa butter ki yanka albasarki ki soya sama sama, sai ki dauko namanki da ki ka yanka ki sa a ciki ki juya kidan bashi tsoro (ki soya sama sama).
 4. Sai ki dauko tarugu ki sa, maggi (iya dandano da zai miki) kayan kamshi ki sa a ciki sai ki sa ruwa kamar cokali uku ki juya sai ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye sai ki sauke ki ajiye a gefe.
 5. Ki dauko shawarma bread naki sai ki dauko kabejin, albasa, tumatur da carrot naki (wanda ki ka gyara a baya) ki sa a gefen shawarma bread din (karki sa a tsakiyan don ya miki dadin nadewa) sai ki dauko namanki (wanda ki ka hadashi a baya) ki sa a gefen su kabejinki (amma naman ya fi su kabejin yawa) sai ki nade Kamar nadin tabarma. Sai ki sa a plat.

Ana iya cinsa tare da shayi ko abu mai sanyi (kamar su lemon kwalba). A ci dadi lafiya

Karin bayani

Za ki iya hada mayonnaise da tomato ketchup a wani kwano daban sai ki shafa a jikin shawarma bread din(kamar yanda ake shafa butter bread) kafin ki jera su kabejin da nama ko kuma ki yaryada akan naman kafin ki nade.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×