Ku karanta yadda ake suya ko tsire a gida a wannan recipe.
Abubuwan hadawa
- Nama (marar kitse)
- Yaji (ki sa Kayan qamshi Kamar su citta, kaninfari Maggi, daddawa, da saukan kayan kamshi da kike bukata)
- Man miya (veg oil)
- Albasa
- Garin citta
- Maggi (na ruwa)
- Gishiri
- Clingfilm
- Foil paper
- Skewers (toothpicks)
- Koren tattasai
- Yellow tattasai
- Kwakwamba (Cucumber)
- Albasa (na garnishing)
Yadda ake hadawa
- Ki sami namanki, ki wanke ki gyara shi, sai ki yanka shi dogo dogo.
- Sai ki yanka albasa
- Ki kawo su yajin ki da maggi
- Ki dauko garin citta da sauran kayan kamshinki (spices) ki sa a kai
- Sai ki gauraya komai ya shiga jikin sa
- Ki dauko clingfilm Ki Rufe Namanki
- Sai ki sa a fridge ki barshi yayi Kamar awa hudu ko ki barshi ya kwana a fridge.
- Ki dauko marinated namanki ki sa a foil paper saiki sa a preheated oven ki gasa shi kamar na minti 30.
- Sannan sai ki fitar Daga oven ki baxa shi ya sha iska, sai ki yan yanka shi.
- Sai ki dauko yajinki da Maggi mai ruwanki ki kara sawa akai ki dauko tsinken nama ki gera su a jiki sai ki yaryada kadan a jikin nama sannan ki Mayar oven ki gasa (kina juyawa don kar ya kone ta gefe daya ). Ga wacce ba ta da oven kuma, za ki iyi daura non.Stick pan naki akan wuta ki gasa.