Skip to content

Yadda ake soyayyen dankali da kwai

Share |
Yadda ake soyayyen dankali da kwai

Mu koyi yadda ake soyayyen dankali da kwai . Wannan soyayyen dankali da kwai yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

 • Dankalin turawa
 • Kwai (3)
 • Man gyada
 • Albasa (1)
 • Attarugu (2)
 • Tumatur (2)
 • Maggi (2)
 • Gishiri

Yanda ake hadawa

 • Da farko dai uwargida za ki fere dankalinki ki yanka dogo-dogo.
 • Sai ki dora kaskonki a wuta ki sa manki yayi zafi sai ki dauko dankali kisa gishiri kijuya kisa a man. Karki yawaita juyashi zai fashe.
 • Idan yayi sai ki tsame amatsami. Yayin da man jikin dankalin ya dige, sai ki sa a kwano mai kyau ki ajiye a gefe.
 • Bayan nan sai ki dauko kwano mai kyau ki fasa kwanki.
 • Sai ki yanka albasarki da attarugu da tumatur, yanka kanana ki zuba a cikin kwai din, sannan ki sa maggi sai ki kada ya kadu sosai.
 • Sai ki dora kaskonki a wuta ki sa mai kadan ki soya sai ki dora kan dankalinki.

Sai a baiwa maigida da yara su yi buda baki da shi. Na gode

Add to Lists (0)

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page