Skip to content

Yadda ake sarrafa gasashshen kifi

Share |
yadda ake sarrafa gasashshen kifi

Uwargida mu koyi yadda ake sarrafa gasashshen kifi. Wannan gasashshen kifi yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

 1. Kifi (babba guda daya ko biyu)
 2. Attarugu 3
 3. Maggi 3
 4. Albasa 2
 5. Tafarnuwa
 6. Cittah
 7. Kori ko kayan kamshi

Yadda ake hadawa

 1. Da farko zaki wanke kifinki ki tsaga gefe ki cire dattin ki saka a frying pan mai dan girma, idan kuma kina da oven shikenan.
 2. Sai ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa ki zuba a wani kwano sai ki zuba mai da maggi da kori ko kayan kamshi sai ki juya komai ya hadu.
 3. Sannan sai ki shafa a jikin kifin ko ina ya samu. Zaki iya tsagashi don ko ina yaji kayan hadin.
 4. Sai ki dora agaushi ko kisa a oven. Ki sa wuta kadan ki dan barshi na yan mintuna kina yi kina juyawa.
 5. Idan yayi sai ki sauke ki tsire kisa a plate, idan kina bukata zaki iya soya dankali ki hada a ci dashi.
Add to Lists (0)

No account yet? Register

2 thoughts on “Yadda ake sarrafa gasashshen kifi”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page