Skip to content

Yadda ake sandwich

Share |
Yadda ake sandwich
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake sanwich mai kyau da kuma alfarma. Wannan recipe ne mai saukin bi ga kuma dadi. Cikin ‘yan lokaci kalilan uwargida za ki hada.

Abubuwan hadawa

 1. Slice bread (biredi me yanka yanka)
 2. Kwai
 3. Butter
 4. Dafaffafen kwai
 5. Tomato ketchup (Tumatur na kwalba)
 6. Latas
 7. Tumatir
 8. Albasa
 9. Maggi
 10. Tarugu
 11. Kayan kamshi

Yadda ake hadawa

 1. Ki gyara latas naki ki wanke da gishiri kadan (ki tsane), ki yanka dafaffafen Kwanki round, albasa ki yanka, tumatir dinki shima ki yanka. Sai ki ajiye a gefe.
 2. Ki fasa kwanki a cikin wani karamin kwano sai ki yanka mishi albasa ki sa tarugu (jajjagen tarugu ko yankakke) sai ki sa maggi, gishiri, kayan kamshi ( iya dandanon da zai miki), sai ki ajiye a gefe.
 3. Dauko bread naki ki sami cookie cutter ko wani karamin abu me round baki (kamar kofi haka) ki yanka tsakiyan sai ki shafa butter a jikinsa. Haka za ki yi har ki gama da sauran bread naki.
 4. Daura non stick pan akan wuta idan ya yi zafi sai ki dauko beredinki ki sa. Sai ki dauko kwanki (wanda ki ka fasa ki kasa su maggi) ki sa kamar cokali 2 a tsakiyan biredinki sai ki gasa , idan kinga alamar ya yi, sai ki juya dayan gefe shima ki gasa. Haka za ki yi da sauran har ki gama.
 5. Daga karshe sai ki dauko biredinki (wanda ki ka gasa da kwai) ki sa a plate. Sai ki dauko latas ki shinfida akan biredin ki kawo su tumatir, albasa, wan da kika yanka ki sa akai latas sai ki yaryada tumatir na kwalba (tomato ketchup) a kai sai ki kawo wani biredin ki rufa akai. Shi ke nan sandwich na ki ya hadu. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake sandwich”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×