Skip to content

Yadda ake samosa

Share |
yadda ake samosa
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake samosa. Wannan samosa din yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

 1. Fulawa (flour)
 2. Kwai
 3. Nama
 4. Maggi
 5. Onga
 6. Kori (Curry)
 7. Gishiri
 8. Man gyada
 9. Attarugu
 10. Albasa
 11. Karas (carrot)
 12. Baking powder

Yadda ake hadawa

 1. Da farko zaki wanke namanki ki tafasa shi da albasa da maggi da gishiri da dan korinki. Ki yi shi tamkar danbun nama.
 2. Sai ki goga karas din ki, ki kuma soya shi
 3. Sai ki zuba fulawarki a roba ki saka baking powder da dan gishiri ki kwaba. Ki murza ta murzu sosai ta yi fadi.
 4. Sai ki rika yankawa kina zuba namanki da karas kina nadewa kamar dan kwali
 5. Sai ki dora mangyadarki a wuta ya yi zafi
 6. Idan yayi zafi sai ki dinga jefa nadadden samosanki kina kisoyashi

Rate the recipe.

Average: 4.2 / 5. Rating: 11

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake samosa”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading