Uwargida ki koyi yadda ake royal chips mai dadi da alfarma. Wannan recipe ne da uwargida za ki hada shi cikn kalilan lokaci.
Abubuwan hadawa
- Dankalin turawa (soyayye)
- Kabeji (a yanka, a wanke)
- Kayan ciki (dafaffe)
- Tarugu (jajjaga)
- Karas (ki yanka)
- Albasa
- Lawashi
- Butter
- Maggi
- Kayan kamshi
Yadda ake hadawa
- Daura tukunya akan wuta ki sa butter ki yanka albasarki ki soya sama sama. Sai ki dauko tarugu ki sa ki soya sama sama, kayan kamshi, maggi ki sa iya dandano da zai mi ki, sai ki juya ki sa ruwa kadan ki rufe nadan wani lokaci.
- Dauko kayan ciki ki sa ki juya, rufe nadan wani lokaci.
- Dauko kabejin, karas, lawashi, ki sa ki juya, rufe nadan wani lokaci sai ki dauko soyayyen Dankalin turawa ki sa ki juya nadan wani lokaci har sai ya hade jikansa. Sai ki sauke ki zuba a plate. A ci dadi lafiya.
Ana iya cin royal chips don karin kummalo (breakfast) a hada da kunun waken soya ko kunun gyada ko shayi da dai duk abin da mutum ke bukata. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba bi izinillahi.