Skip to content

Yadda ake puff-puff (Fanke)

Share |
Yadda ake puff puff (Fanke)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Barkanmu da sake saduwa a fanninmu na girke girke a dandalin Bakandamiya Kitchen. A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake puff-puff ne, da fatan mai karatu za ta amfana da wannan sabon darasin. Sannan za a iya duba girkinmu na baya inda muka koyar da Yadda ake Japanese Pancake kafin mu ci gaba.

To ga yadda ake puff-puff nan dalla dalla kamar haka:

Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Yeast
  3. Sugar
  4. Gishiri kadan
  5. Mangyada
  6. Ruwa
  7. Madarar ruwan
  8. Kwakwa

Yadda ake hadawa

  1. Ki sami babba kwano ki tankade filawanki a a ciki ki zuba yeast, sugar, gishiri kadan ,ruwan madarar kwakwa ki tare da ruwa (ruwan dan daidai za ki sa domin kinsa madarar kwakwa a ciki).
  2. Sai ki kwaba kullin (kar ya yi ruwa kuma ba kauri ri sosai ) daga nan ki sa shi a rana kamar minti 20 ya tashi.
  3. Da zarar ya taso, sai ki sake bugashi sosai sai ki daura kaskonki a kan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama idan ya yi zafi kina diba kadan kadan kina soyawa har sai ya soyu sai ki tsane a matsani. A na iya cinsa da Nutella (chocolate) Ko da jam ko haka nan da tea. A ci dadi lafiya.

 Wannan shine yadda ake puff-puff. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×